150318-za-a-gudanar-da-dandalin-nahiyar-asiya-na-boao-a-karshen-wannan-wata-bello.m4a
|
Za a shirya taron shekara-shekara na dandalin nahiyar Asiya na Bo'ao, daga ranar 26 zuwa ta 29 ga watan Maris na shekarar da muke ciki, a birnin Bo'ao dake lardin Hainan na kasar Sin.
Taron da aka yiwa lakabi da "sabuwar makomar nahiyar Asiya: Yunkurin samar da kakkarfar al'umma domin cimma moriyar bai daya".
Babban magatakardan dandalin nahiyar Asiya na Bo'ao, mista Zhou Wenzhong, ya kira taron manema labaru a nan birnin Beijing a ranar Talata 17 ga wata, inda ya yi bayani game da share fagen taron na dandalin Bo'ao na wannan shekara, gami da tsarin taron. Mista Zhou ya ce,
"Ban da shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda zai halarci bikin budewar taron, akwai sauran shugabannin kasashe daban daban da za su halarci taron na bana, na dandalin nahiyar Asiya na Bo'ao. Gwamnatin kasar Sin wadda ita ce mai masaukin bakin taron, za ta gabatar da sunayen mahalartan nan da 'yan kwanaki masu zuwa. Abin da muka sani shi ne, za a samu shugabannin kasashe daban daban da za su halarci taron a wannan karo, wadanda yawansu zai wuce na baya."
A cewar mista Zhou, wasu manyan kusoshin gwamnatoci fiye da 2000, wadanda suke kula da harkokin siyasa, da cinikayya, da harkar ilimi, da watsa labaru, za su halarci taron na bana, inda za su gudanar da tarurukan tattaunawa 77, kuma dukkanin tarukan za su jibinci babban taken taron na 'sabuwar makomar nahiyar Asiya: Yunkurin samar da kakkarfar al'umma domin cimma moriyar bai daya". Kana abubuwan da za a tattauna za su shafi bangarori 6, wato manyan tsare-tsaren tattalin arziki, da hadin gwiwa a yankuna daban daban, da sauya salon masana'antu, da kirkiro sabbin fasahohi. Sauran su ne tsaro a fannin siyasa, da zaman rayuwar jama'a, inda za a fi maida hankali kan batun hadin gwiwar da ake yi a yankuna daban daban.
"An dade ana mai da hankali kan hadin gwiwa a yankuna daban daban a tarurukan da muka shirya a baya. A shekarun baya, ana kokarin sa kaimi ga hadin gwiwar da ake yi a nahiyar Asiya. La'akari da wannan yanayi da ake ciki, ya sa muka zabi wasu batutuwan da aka fi maida hankali kansu, domin a gudanar da jawabai da tattaunawa a kan su, kuma za mu gayyaci shugabannin da batutuwan suka shafa domin su halarci bukukuwan da za a shirya."
Haka zalika, an ce, wani abun da zai fi janyo hankali a wannan taron, shi ne kokarin kirkiro sabbin fasahohi da kafa kamfanoni. A wajen taron, mista Bill Gates, mai kamfanin Microsoft, gami da wasu masu masana'antu, za su yi musayar ra'ayoyi dangane da fasahohi, da kokarin kirkiro sabbin fasahohi, gami da batun samun ci gaba mai dorewa. Ban da haka kuma, wasu kwararru a fannin yanar gizo ta Internet na kasashe daban daban, za su zanta, tare da manyan kusoshi na fannonin hada-hadar kudi, da fannin cinikayyar gidaje, da kayayyakin lantarki, da dai sauransu.
A matsayin wani dandalin tattalin arziki mafi tasiri a nahiyar Asiya, dandalin nahiyar Asiya na Bo'ao ya fara taka rawar gani a fannin samar da hanyoyin da za a bi domin warware matsaloli.
A yayin taron manema labarun da aka shirya a ranar Talata, hukumar dandalin nahiyar Asiya na Bo'ao ta fitar da rahotanni guda 3, wadanda suka shafi fannonin dunkule tattalin arzikin kasashen Asiya waje daya, da karfafa nahiyar Asiya a fannin takara, da sauran yankunan duniya, gami da ci gaba da sabbin hanyoyin bunkasa tattalin arzikin da ke bullowa cikin sauri.
A wajen taron, shahararren masanin tattalin arzikin kasar Sin Wang Jun, wanda ya kula da aikin tsara rahoto game da karfin nahiyar Asiya wajen takara da sauran yankuna daban daban, ya gabatar da jerin sunayen kasashen nahiyar Asiya, wanda ya bayyana matsayin kasashen a fannin samun karfin takara da sauran kasashe. A cewarsa, kasar Sin tana matsayi na 9 cikin kasashe da yankuna 37 dake nahiyar Asiya, matsayin da ya yi daidai da wanda take kai a bara.
Ban da haka kuma, mista Wang Jun ya ce, yayin da tattalin arzikin nahiyar Asiya ke karuwa cikin sauri a shekarar 2014, kasashen nahiyar na kara fuskantar rashin tabbas dagane da ci gaban tattalin arzikinsu. Ya ce,
"Ana kara ganin yiwuwar fuskantar wasu hadaruruka, wadanda za su kunshi yadda ake kara samar da ruwan bashi a Amurka. Yayin da wasu kasashe ke matukar dogaro kan samun bashi daga kasashen waje, kamar su Indiya da Indonesiya. A daya hannun kuma wasu kasashen na da jarin kasashen waje da yawa cikin kasuwanninsu na hada-hadar kudi. Wadannan kasashe za su yi kokarin takaita bashin da ake binsu a shekarar 2015." (Bello Wang)