in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana sun yi hasashen bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin da kaso 7% a badi
2014-12-17 17:36:27 cri

A halin yanzu tattalin arzikin kasar Sin ya shiga wani sabon tsari na bunkasuwa. A ganin masana ilmin tattalin arziki da dama, yadda tattalin arzikin kasar Sin ke bunkasa yana sauyawa daga saurin gaske, zuwa wani matsakaicin matsayi, duk da cewa akwai dimbin kalubale da ake fuskanta, a hannu guda akwai kuzarin da ke cikin bunkasuwar tattalin arzikin kasar ta Sin. Don haka ne masanan ke hasashen cewa, saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar ta Sin zai kai ga kimanin kashi 7% a shekara mai zuwa.

A gun wani taron shekara shekara na masana ilmin tattalin arziki da aka gudanar a kwanan baya, wani mashahurin masanin ilmin tattalin arzikin kasar Sin, kana shehun malami a jami'ar Peking, Mr. Li Yining ya bayyana cewa, ma'anar sabon tsarin shi ne, gudanar da abubuwa bisa dokar gudanar harkokin tattalin arziki. Ya ce, a shekarun da suka gabata, yadda tattalin arzikin kasar Sin ke bunkasa da saurin gaske bai dace ba, haka kuma ba zai dore ba, sabo da hasarorin da hakan ke haddasawa masu yawa, ya ce, "wadanne hasarori ne suka faru? Na farko akwai lalacewar alkarbatun kasa. Na biyu, gurbacewar muhalli. Na uku, rashin ingancin aiki. Na hudu, kayayyakin da aka samar sun wuce abin da ake bukata. Banda haka ma, abu mafi muhimmanci shi ne damar yin kirkire-kirkiren fasahohin zamani, da kuma gyaran tsarin da a baya ya subucewa kasar Sin.

A shekarar 2008, yayin da manyan kasashe masu sukuni ke kokarin kirkiro sabbin fasahohi, da kuma gyaran tsare-tsaren su, kasar Sin a maimakon daukar wannan mataki ta mai da hankali ne kawai a kan samun saurin bunkasuwar tattalin arziki, sai dai abin da ta samu bai biya hasarar da ta yi ba."

Masanin ya kara da cewa, sabon tsarin da aka shiga shi ne na daidaita saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin zuwa wani matsakaicin matsayi, tare da mai da hankali kan kara ingancin tattalin arziki, da kuma daidaita tsarinsa. Har wa yau ya bayyana wasu ra'ayoyi da suka shafi bunkasuwar tattalin arziki, da ya kamata a tabbatar da sauye-sauyensu. Ya ce, "Na farko, tsarin tattalin arziki ya fi GDP muhimmanci, na biyu, ya kamata a daidaita ra'ayoyi kan yadda ake fitar da kayayyaki da shigowa da kayayyaki, sabo da ba lalle bane karin fitar da kayayyaki zuwa ketare ya iya haifar da alfanu. Na uku, ba lalle bane yawan samar da guraben aikin yi, ya kasance yana da alaka da yawan zuba jari. Na hudu, babu tabbas cewa yawan kudin ruwa zai iya dakile hauhawar farashin kaya. Na biyar, ya kamata a gane cewa ana iya kirkiro kasuwa."

Har wa yau a wajen taron, tsohon ministan kudin kasar Amurka, kuma tsohon shugaban jami'ar Harvard, Mr. Larry Summers ya bayyana cewa, a cikin shekaru 35 da suka wuce, zaman rayuwar al'ummar kasar Sin ya inganta kwarai da gaske, kuma bunkasuwar tattalin arzikin kasar ma ya habaka. Duk da haka, ya yi nuni da cewa, akwai kalubale da dama da ke gaban kasar ta Sin, wadda ta kai wani lokaci na kawo sauye-sauye. Ya ce, "kasar Sin ta kai wani lokaci na kawo sauye-sauye, musamman a cikin gida, ta karkata akalarta zuwa bukatun gida sabanin yadda take fitar da dimbin kayayyaki zuwa ketare, zuwa fadada tattalin arziki masu zaman kansu, sabanin yadda kaso mai yawa na fannin tattalin arzikinta ke karkashin mallakar gwamnati. Ban da haka, ta kara mai da hankali a kan kiyaye muhalli, yayin da take bunkasa tattalin arzikinta."

Baya ga haka, Qiu Xiaohua, wani babban masanin ilmin tattalin arziki ya yi hasashen cewa, nan da shekaru 10 masu zuwa, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin zai kai ga a kalla kashi 7%. Ya ce, "nan da shekaru 10 masu zuwa, ba abu ne mai wuya ba, a samu bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin da zai iya kaiwa kashi 7%. Har yanzu kuzarin bai kare ba, ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, kuma masana'antu da birane, da sadarwa da dunkulewar shiyyar, da aikin gona, su ne manyan fannonin da aka sanya muhimmanci wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Sin. Amma, kasar Sin ba ta kammala kashi 2/3 ba na aikin bunkasa masana'antunta ba, haka kuma ba ta kai rabi ba wajen bunkasa biranenta. Baya ga haka, kasar Sin ta zo daya da kasashen duniya wajen bunkasa harkokin sadarwa, kuma ba ta yi nisa ba, wajen tabbatar da dunkulewar shiyyar, da kuma bunkasa aikin gona na zamani ba. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China