A Liberiya an sanar da karshen yaduwar cutar ne tun a ranar 9 ga watan Mayu amma kuma sai cutar ta sake bulla a ranar 29 ga watan Yuni inda aka samu wassu masu dauke da ita su 6.
A karkashin bincike da sa ido da ake yi gwamnatin Liberiya cikin sauri ta dauki matakin dakile sabon bullowar cutar. Hukumar ta WHO ta jinjina ma gwamnatin kasar tare da al'ummar ta bisa ga wannan nasara tana mai tabbatar da cewa za ta ba da dukkan taimakon da ya wajaba a cikin kwanaki 90 na matakin koli na binciken cutar da kuma kokarin ganin saurin farfadowar kasar. (Fatimah Jibril)