Hukumomin kiwon lafiya a kasar Saliyo sun tabbatar a ranar Lahadi cewa, an gano wani sabon mutumin dake dauke da cutar Ebola a yankin Kambia dake arewacin kasar. Wannan diya ce ga wata mace mai shekaru 67 da haifuwa da ta mutu baya bayan nan sanadiyyar cutar Ebola a garin Sellakafter, dake kusa da kan iyaka da kasar Guinea.
A cewar Abbas Kamara, jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar kiwon lafiyar kasar, sakamakon gwajin jini kan wannan maras lafiya ya nuna cewa, tana dauke da cutar. Gano wannan mata mai dauke da cutar Ebola na tabbatar da wa'adin kwanaki 42 na kawo karshen cutar ko a'a. (Maman Ada)