Kakakin hukumar Yayah Tunis ya shaida ma kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua cewa, duk mutane ukun da aka tabbatar sun kamu da cutar sun fito ne daga kauyen Sellakafter, kuma 'yan uwa ne na jiki ga wata tsohuwa 'yar shekaru 67 da ta rasu sakamakon cutar a kauyen.
Yanzu wannan adadin ya zama mutane hudu ke nan da aka tabbatar suna dauke da cutar a kasar baki daya, sannan dukkansu an riga an killace su don hana yaduwar cutar.
Yayah Tunis da yake karin haske a kan al'amarin ya ce, yanzu haka dangin marigayiyar na daga cikin mutane 50 dake fuskantar hadari matuka a kauyen, kuma hukumar tana lura da su kwarai, ya ce duk da dai su ma sun damu amma ya fi sauki a kebe su tun da an riga an killace gidan da suka fito ainihi.
Ya jaddada sakon hukumar ga al'umma da su kiyaye ka'idoji na tabbatar da ba su taba ko wanke jikin mamaci ba, kuma su kira cibiyar kula da aikin hana yaduwar cutar cikin gaggawa idan danginsu ya kamu da rashin lafiya.
Ya bayyana cewa, hukumar ta kara aikawa da karin jami'ai a yankunan da cutar ta bulla duk a cikin kokarin wayar da kan jama'a.(Fatimah Jibril)