A jiya Litinin ne dai wani jami'in watsa labaru a cibiyar lura da cutar Ebola dake kasar ta Saliyo Yaya Tunis, ya bayyanawa majiyar mu cewa, an tabbatar wannan mata yar shekaru 60 a duniya ta kamu da cutar Ebola ne bayan ta rasu kafin a yi mata jana'iza. Kafin hakan an shafe kwanaki 50 ba a gano sabbin masu kamuwa da cutar ba a yankin Kambia inda matar take da zama.
Jami'in ya kara da cewa, an riga an kebe mutane 10 da suka yi cudanya da wannan mata, kana kungiyoyi biyu na gwamnatin kasar sun soma bincike kan asalin cutar, ba kuma da jimawa ba za a tsaida kuduri kan ko za a killace dukkanin al'ummar da wannan mata ke zaune da su ko a'a. (Bilkisu)