Kafin lambar tagullar da Katende ya samu, shi ma dan wasan badminton na kasar Edwin Ekiring, ya lashe irin wannan lamba a wasan kusa da na karshe ajin maza da ya buga shi da dan kasar Afirka ta kudu wanda yayi nasara a wasan.
Duk dai da matsayin da 'yan wasan na Uganda suka samu bai kai matakin koli ba, Katende ya ce yayi farin ciki da tagullar da ya samu. Ya ce gwabzawar da suka yi da takwaransa na Algeria ta bashi damar sake gogewa, tare da sake fahimtar dabarun wasan na dambe.
Benchelba Abdelhafid na Algeria ya taba kaiwa wasan zagayen gasar har sau biyu a baya. Da kuma wannan nasara ta lashe lambar tagulla da 'yan Ugandan biyu suka samu, kasar ta daga zuwa matsayi na 20 sama da kasar Mali da tagulla biyu, yayin da kuma Masar ta ci gaba da mamaye gasar da lambobi 130 wadanda su ne mafiya yawa a gasar, kana Afirka ta Kudu ke biye mata a matsayi na biyu.(Saminu Alhassan)