in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An garzaya da shahararran dan wasan tseren mita 400 Niekerk zuwa asibiti
2015-08-27 11:13:27 cri
An garzaya da dan wasan tseren gudun mika 400 nan da ya kafa sabon tarihi a duniya Wayde van Niekerk zuwa wani asibiti mafi kusa bayan da ya yanki jiki ya fadi, yayin da dan wasan ke fafutukar neman yin nasara a gasar tseren duniya da ake gudanarwa a Katafaren filin wasa na kasar Sin dake birnin Beijing a ranar larabar nan.

Likitan da ya duba dan wasan wanda kuma dan asalin kasar Afrika ta kudu ne ya tabbatar da cewar yana fama da matsalar daukewar numfashi.

Van Niekerk wanda ya samu nasara a gasar tseren mita 400 yayi nasarar ne ciki da makin dakika 43.48 kuma shine na hudu cikin 'yan wasan da suka fi samun kwarewa a tarihin wasan.

Dan wasan yana gaba da Lashawn Merritt dan kasar Amurka da ya yi nasara sau biyu a gasar motsa jiki ta Olymphic a shekarar 2008 da gasar motsa jiki ta duniya kuma shine na biyu da makin dakika 43.65 a wannan karo, yayin da Kirani James wanda ya zama zakara a gasar motsa jiki ta duniya ta shekarar 2011 da gasar Olymphic ta shekarar 2012 ya kasance na uku da makin dakika 43.78. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China