150820-fitattun-yan-wasa-da-za-su-nuna-kwarewa-a-gasar-wasannin-tsalle-tsalle-da-guje-gije-ta-beijing-bello.m4a
|
Ma iya cewa, a fannin wasannin tsalle-tsalle da guje-guje, dan wasan da ya fi janyo hankalin jama'ar duniya shi ne Usain Bolt daga kasar Jamaica, wanda ake masa lakabin "Walkiya", ganin yadda ya yi fice a fannin tseren mita 100, da na mita 200. A lokacin gasar wasannin Olympics na shekarar 2008 wadda ita ma ta gudana a nan birnin Beijing, shi Bolt ya karya matsayin bajinta da ake rike da shi a wasanni 3, yanzu ga shi zai sake komowa birnin Beijing, inda ya taba samun manyan nasarori, tare da niyyar karya matsayin bajinta na daban.
An ce ko da lambar zinariya guda daya tak ya samu a wannan karo, hakan zai sa yawan lambobin zinariyan da ya taba samu a gasar wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ajin kwararru ya wuce guda 8, jimillar da za ta wuce matsayin bajimtar da fitattun 'yan wasan Amurka Carl Lewis, da Michael Johnson suke rike da su.
Hakika dai samun lambar zinariya daya tak ma ba abu ne mai sauki gare shi ba, ganin yadda Bolt din ba ya cikin wani yanayi mai kyau matuka a wannan kakar wasa, inda ya kammala tseren mita 100 cikin dakika 9.87. Yayin da a daya hannun a wannan kakar wasa aka samu 'yan wasa 5 da suka fi shi sauri, wato 'yan wasa kamar su Justin Gatlin, da Trayvon Bromell na kasar Amurka, da abokin kungiyar Bolt Asafa Powell, da Keston Bledman, wanda ya zo daga tsibiran Trinidad da Tobago, gami da dan kasar Faransa Jimmy Vicaut, wadanda dukkansu za su halarci gasar da za ta gudana a nan Beijing.
Sai dai tawagar Jamaica ba za ta dogara kan Bolt kadai wajen neman samun lambobi ba, ta la'akari da dimbin yawan fitattun 'yan wasan guje-guje da ke cikin tawagar kasar. Ga misali, Shelly-Ann Fraser-Pryce, 'yar wasan da ta lashe lambobin zinariya 3 a gasar IAAF ta birnin Moscow a shekarar 2013, duk da cewa ta ce za ta kaurace wa tseren mita 200, amma ga alama hakan zai sa ta dukufa kan tseren mita 100, da tseren mita 100-100 na 'yan wasa 4.
Cikin tawagar Najeriya kuwa, akwai fitacciyar 'yar wasan da za ta iya gwada sa'ar ta da Fraser, sunanta Blessing Okagbare, wadda a gasar IAAF da ta gudana a birnin Moscow a shekarar 2013, ta taba lashe lambar azurfa a wasan tsalle, gami da lambar tagulla a tseren mita 200. Sa'an nan a watan Mayun bana, Blessing ta lashe Fraser a tseren mita 100, ta kuma ci lambar zinariya a wata babbar gasar da ta gudana a birnin Shanghai na nan kasar Sin.
A daya bangaren, gabanin gasar da za a yi a Beijing, shugabannin hukumar wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta Najeriya sun ba ta shawarar kara dukufa kan wasa 1 ko 2, domin neman samun lambar zinariya, duk da cewa ta kware a fannoni daban daban kamar su tseren mita 100, da 200, da wasan tsalle.
Sauran 'yan wasa mata da suka yi fice a fannin guje-guje sun hada da English Gardner na kasar Amurka, wadda ta kware a wasan tseren mita 100, gami da Allyson Felix, wadda ta taba lashe lambar zinariya a wasannin Olympics na birnin London na shekarar 2012, a wasan tseren mita 200.
A fannin wasan tseren mita 400 na maza, Isaac Makwala na kasar Botswana, da Kirani James na tsibirin Grenada, da Wayde van Niekerk na kasar Afirka ta Kudu, dukkan su sun taba kammala tsere cikin dakikoki 44. Yayin da a bangaren mata, Francena Mccorory ta kasar Amurka, da Shaunae Miller ta kasar Bahama, duka sun taba kammala tseren mita 400 cikin dakika 50. Haka kuma a wasan tseren mita 800, wanda yake rike da matsayin bajimta a wannan wasa shi ne Rudisha David Lekuta daga kasar Kenya, wanda shi ma zai halarci gasar nan ta birnin Beijing.
Sa'an nan a fannin gudun matsakaici da dogon zango, wanda ya fi janyo hankali shi ne dan wasan Birtaniya Mohammed Farah, dan asalin kasar Somaliya. Wannan dan wasa a gasar Olympics ta birnin London ya lashe lambobin zinariya a tseren mita 5000 da na 10,000. A kakar wasa ta bana kuwa, ya kiyaye matsayin fifiko a tseren mita 10,000, amma a fannin tseren mita 5000 zai fuskanci kofar rago daga kwararrun 'yan wasan kasar Habasha da suma zasu shiga a fafata da su.
A gasar gudun dogon zango na yada-kanin-wani, ana sa ran ganin 'yan wasan kasashen Kenya da Habasha masu matukar hazaka kamar yadda suka saba nunawa. A wannan bangare Mare Dibaba ta kasar Habasha ta lashe lambar zinariya a gasar gudun Marathon da aka yi a farkon shekarar nan ta bana a birnin Xia'men dake kudancin kasar Sin, inda ta karya matsayin bajinta da ake rike da shi a wannan gasa. Yayin da shi kuma dan wasan kasar Kenya Dennis Kipruto Kimetto, ya kafa tarihi a bara, inda ya zama mutum na farko da ya kammala tseren yada-kanin-wani cikin sa'o'i 2 da mintuna 3.(Bello Wang)