A jiya Litinin ne, mataimakiyar darektar hukumar kula da harkokin mata da yara ta majalisar gudanarwar kasar Sin Song Xiuyan ta sanar a gun bikin bude taro karo na 59 na hukumar kula da harkokin mata ta MDD cewa, kasar Sin za ta shirya taron koli na mata na duniya tare da hukumar kula da harkokin mata ta MDD a watan Satumba na wannan shekara. Kuma ana saran shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron, inda zai ba da jawabi.
Madam Song Xiuyan ta ce, shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 20 da fara shirya taron mata na duniya, kasashe daban daban sun samu sakamako mai kyau a fannonin tabbatar da adalci a tsakanin maza da mata da kara baiwa mata 'yanci, amma duk da haka suna ci gaba da fuskantar matsaloli da kalubale. A watan Satumba na wannan shekara ne, kasar Sin za ta kira taron koli na mata tare da MDD a lokacin da ake shirya jerin tarurukan koli na MDD a birnin New York.
Haka kuma, Madam Song Xiuyan ta ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping da babban sakataren MDD Ban Ki-Moon za su gayyaci shugabannin kasashe membobin MDD da su halarci taron. Ta yadda za a ingiza kasashe daban daban da su tabbatar da "Sanarwar Beijing" da "Tsarin gudanar da aiki" domin yin sabon alkawarin siyasa da samar da taimako kudin cimma burin raya harkokin mata bayan shekarar 2015.(Lami)