in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta lashe gasar kwallon Kwando ta kasashen Afirka 4
2015-03-26 14:27:24 cri
Kulaf din D'Tigers na kwallon Kwando dake tarayyar Najeriya, ya lashe gasar kwallon kwando ta bana, mai kunshe da kasashen Afirka 4, wadda aka kammala a kasar Afirka a Lahadin karshen mako.

A karshen gasar dai D'Tigers ta doke kulaf din kasar Mozambique da maki 72-59, a zauren wasa na Wembley dake birnin Johannesburg.

Kafin hakan dai sai da D'Tigers ya samu nasarar wasan sa da kulaf din kasar Afirka ta Kudu da maki 97-58, a wasan su na farko na ranar Juma'a, kafin kuma ya lallasa kulaf din kasar Kenya da maki 83-52 a ranar Asabar.

A wasan daf da na karshe kuwa D'Tigers ya baiwa Mozambique ruwa da maki 51-42 a ranar ta Asabar, kafin haduwar su ta karshe a ranar Lahadi.

Rahotanni sun nuna cewa kaftin din kungiyar D'Tigers Olumide Oyedeji ya baiwa 'yan wasan sa cikakkiyar gudummawa, da kwarin gwiwa wajen lashe dukkanin wasanni 4 da suka lashe, matakin da ya ba shi damar karbar lambar yabo ta dan wasa mafi daraja a gasar.

Bayan komawar 'yan wasan na D'Tigers gida, ana sa ran za su shiga shirin tinkarar kasar Burkina Faso, a wasan zagaye na biyu, na zangon karshe na share fagen gasar FIBA ta nahiyar Afirka, wadda ke tafe nan gaba cikin wannan shekara, gasar da kuma ake yiwa lakabi da Afrobasket.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China