in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta sake zama zakarar kwallon Kwando ta duniya
2014-09-19 10:20:52 cri

Kasar Amurka ta kare kambin ta na kasancewa zakarar kwallon kwando ta duniya, bayan da a ranar Lahadin makon jiya kulaf din kasar ya doke takwaransa na Sabia da maki 129 a wasan karshe da suka kara a filin wasa na Palacio de Deportes dake birnin Madrid.

A ganin wasu manazarta harkokin wasanni dai Kulaf din na Amurka ya gaza taka rawar gani irin wadda ya yi shekarar 1994, inda ya kammala wasan sa na karshe da maki 137, ya yin da shi kuwa kulaf din kasar Sabia ya yi iyakacin kokarin lashe kofin na wannan kari, ko da yake hakan bata samu ba.

Duk dai da kallon gazawa da wasu ke yiwa kulaf din na Amurka a bana, ya samu gagarumar nasara a wasannin da ya buga, ciki hadda lashe dukkanin wasannin sa 9 na karshe da gagarumin rinjaye.

Kafin wasan na karshe dai Amurka ta doke Mexico da maki 86 da 63, ta kuma baiwa Slovenia mamaki, inda suka ta shi wasan su da maki 119 da 76. Sai kuma wasan quarter finals, inda Amurkan ta lallasa Lithuania da maki 96 da 68.

A kuma wasan karshe da Amurkan ta doke Sabia, an kai ga maki 35 da 21 a zangon farko na wasan. Kafin a kuma dora zuwa maki 67 da 41 a hutun rabin lokaci. Kana kulaflikan biyu sun kai ga cimma maki 105 da 67 mintuna goma a hura tashi daga wasan. Daga karshe dai Amurkan ta kara yawan makin ta zuwa 129, ya yin da Sabia ta tsaya a maki 92.

'Yan wasan kasar ta Amurka dai sun yi iya kokarin baje kolin bajimtar su ya yin wasannin da suka buga, an kuma ga irin yadda manyan 'yan wasan kasar suka baje basirar su, ciki hadda taurarin kulaf din irin su Kyrie Irving, da James Harding, wadanda suka jefa kwallaye mafiya maki a gasar ta bana.

A daya bangaren kuwa, mai masaukin bakin gasar ta bana wato kasar Sifaniya ta fice ne daga gasar a wasan kusa da na kusa da karshe, bayan da Faransa ta doke ta.

Faransa ce ta uku a gasar kwallon Kwando ta duniya

Har yanzu dai muna kan wannan gasa ta cin kofin kwallon Kwando ta duniya wadda kasar Sifaniya ta karbi bakunci a bana.

Kamar dai yadda muka bayyana, Amurka ce ta lashe gasar ta bana, ta kuma kare lambar ta ta zinari, kana kasar Sabia ta samu lambar Azurfa a matsayi na biyu, ya yin da ita kuma kasar Faransa ta karbi lambar Tagulla a matsayi na Uku, bayan ta doke takwarar ta ta Lithuania da maki 95 da 93, a wasan neman na uku da suka kara ranar Asabar.

Faransa dai ta sha da kyar, bayan da wansan ya kawo karshe, kuma daukkanin bangarorin biyu suka yi ta kokarin ganin sun yi amfani da dukkanin dama wajen lashe wasan a mintunan karshe.

Masu fashin baki dai sun jinjinawa dan wasan Faransa Nicolas Batum, wanda ya taka rawar gani matuka a wasannin da kulaf din ya buga, ciki hadda wasan kusa da na karshe, wanda Sabia ta samu nasara a kan Faransan. A wannan wasa dai Batum ya jefa kwallaye da suka baiwa kulaf din maki har 27, makin da ya baiwa Faransar damar nuna bajimta a zagayen karshe na gasar. Kafin hakan ma kulaf din kwallon Kwando na Faransa shi ne ya fidda kasar Sifaniya a zagayen karshe mai kunshe da kulaflika 8. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China