Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan a jaridar Wall Street Journal. Ya ce, akwai wasu da ke kokarin kawo wa JKS kafar ungulu don haka tilas a samu wasu matsaloli da ba za a rasa ba, lamarin da ya haifar da matsalar cin hanci nan da can.
Don haka ya ce, wajibi ne jam'iyyar ta jajirce domin tunkarar wannan matsala ta hanyar gyare-gyare da tsarkake kai.
Tun a lokacin babban taron jam'iyyar karo na 18, kasar Sin ta karfafa matakan yaki da cin hanci da rashawa, inda aka hukunta manyan jami'an gwamnati da dama da aka samu da laifin cin hanci kamar yadda doka ta tanada.
Shugaba Xi ya ce, yayin da ake kara daukar matakan yaki da cin hanci, gwamnati za ta kara mayar da hankali kan gina tsari mai inganci don ganin cewa, jami'an gwamnati ba su tsunduma cikin halayyar karbar na goro ba.(Ibrahim)