Sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'ar da wata kungiya mai rajin tabbatar da adalci ta tattara ya nuna cewa, sama da kashi 62 cikin 100 na 'yan kasar hankalinsu ya fi karkata ga jam'iyyar CCM mai mulkin kasar fiye da dukkan jam'iyyun siyasun kasar.
Sakamakon kuri'ar jin ra'ayin ya kuma nuna cewa, Jam'iyyar adawa ta CHADEMA ce za ta ci gaba da kasancewa ta biyu, inda dan takararta Edward Lowassa ya samu kashi 25 cikin 100 a kuri'ar jin ra'ayin jama'ar da aka tattara.
A ranar 25 ga watan Oktoba ne al'ummar kasar Tanzaniya za su zabi sabon shugaban kasa da 'yan majalisun dokoki. Kuma 'yan takara 8 ne za su fafata a zaben shugaban kasar. (Ibrahim Yaya)