Hakan a cewar shugaban sashen tsare-tsare da ke kula da gabashin Afirka na asusun, Geofrey Mwanjela, babban lamari ne da zai haifarwa kasar koma baya. A cewar Mwanjela dazukan dake yankin, sansani ne na nau'o'in tsuntsaye da dabbobi kimanin 100, wadanda rashin dajin ke barazana ga wanzuwar su a ban kasa.
A daya bangaren kuma, babban darakta mai kula da Asusun raya tsaunukan na Arc Francis Sabuni, ya ce Asusun sa na gudanar da wani shiri na shekaru 5, wato daga 2011 zuwa 2016, wanda zai bada damar bunkasa dazuzzukan yadda ya kamata. Ya ce karkashin shirin wanda ke samun tallafi daga kasar Norway, ana fatan dakile matsalolin dake haddasa kankancewar albarkatun gadun dazukan. Sabuni ya kara da cewa al'ummun dake rayuwa a kewayen dazukan na dogaro ga noma, da kuma albarkatun daji, wanda hakan ke haifar da matsala ga dorewar dazukan.
Dazukan Arc dake kusa da tsaunukan gabashin kasar ta Tanzaniya dai na da dadadden tarihi, sun kuma kunshi dazuka 13, da suka hade kudancin Kenya zuwa kudu maso tsakiyar kasar ta Tanzania.