Rahotanni daga Tanzania sun nuna cewa mahukutan kasar za su kafa wani rukunin hadin gwiwa tare da hukumomin Sin da abin ya shafa domin cimma nasarar yaki da kayayyakin na jabu da ake shigar da su daga kasar Sin.
Haka zalika kuma, labaran sun tsamo ra'ayin kasar Sin game da wannan ayyuka, inda Sin din a matsayin ta na kasa ta biyu mai karfin arziki a duniya, tana dora muhimmanci kan yaki da kayayyakin jabu, a kokarin kyautata sunan kayayyakin kasar Sin.
Game da hakan ne gwamnatin kasar Sin ta tsaida kudurin gudanar da ayyukan yaki da kayayyakin jabu a kasashen waje, da yakar fitar da kayayyakin jabu daga kasar ta Sin zuwa kasashen waje.
A daya hannun kuma Sin za ta yi hadin gwiwa tare da ma'aikatar masana'antu da cinikayya ta kasar Tanzania, da hukumar kula da kudin haraji, da ofishin 'yan sanda na kasar, da ma sauran hukumomin da abin ya shafa don warware wannan matsala, da kuma tabbatar da samar da kayayyaki masu inganci na kasar Sin ga jama'ar kasar Tanzania. (Zainab)