Ojo-Oba ya shaida manema labarai a Abuja cewa kungiyar 'yan wasannin na kasar ba su da dalilin da zai hana su zama zakara idan aka yi la'akari da matakin shirin da suka yi da kuma irin goyon bayan da mahukuntar kwamitin wasannin kasar ke ba su.
Ya ce ana fatan haka saboda duk wani abin da ya kamata 'yan wasan tare da alkalan wasan duk an tanada musu. Yana mai bayanin cewa yadda kasar za ta yi wasanni 21 akwai tabbacin cewa tana da alamu mai kyau don haka dole ne ta yi nasara.
Wasannin da Nigeriya za ta yi a lokacin gasar wasannin na Afrika sun hada da gudu, kwallon Kwando, kwallon tebur, dauka nauyi, takwandeo, rugby, nunkaya, voli ball, kokuwa, wasan kwallo cikin ruwa, tseren keke, kwallon kafa da kwallon hannu.
Sauran wasannin sun hada da kareti, judo, tseren guragu, dambe, wasan naushi,da gymnastic.
A don haka tsohon Darektan ya bukaci kungiyar 'yan wasannin na Nigeriya da su tabbatar da ba da mamki fiye da wasannin baya na irin wannan gasar da ya guda a birnin Maputu na kasar Mozombique inda ta zo na uku da lambobi 98. (Fatimah)