A jiya ne, a birnin Addis Ababa na kasar Habasha aka kaddamar da hanyar jirgin kasa da kamfanin gina layin dogo na kasar Sin ya gina.
Game da wannan batu, Hong Lei ya ce, yanzu kasashen Afirka suna kara kokarin raya masana'antunsu, haka kuma suna bukatar gaggauta raya manyan ababen more rayuwarsu..
A matsayinta na aminiyar kasashen Afirka, Sin za ta sa kaimi ga yin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu a wadannan fannoni, a kokarin inganta samun ci gaba tare tsakanin Sin da kasashen Afirka, da kuma kawo alheri ga jama'arsu baki daya.
Rahotanni na cewa, wannan ita ce hanyar jirgin kasa mai amfani da wutar lantarki ta farko a kasar Habasha, har ma da nahiyar Afirka dake kudu da Sahara, wadda za ta magance matsalar zirga-zirga da ake fuskanta a hedkwatar kasar.(fatima)