Hifikepunye Pohamba ya bayyana hakan ne yayin da ya halarci taron dandalin tattaunawa karo na 4 tsakanin jama'ar kasar Sin da kasashen Afrika a birnin Yiwu dake lardin Zhejiang na kasar Sin.
Bayan taron, ya bayyana wa wakilinmu cewa, yana fatan kasashen biyu za su inganta hadin gwiwar cinikayya a tsakanin su, kuma jama'ar kasashen Afirka suna son ganin an kara shigar da kayayyakin Sin zuwa kasashensu tare da samun saukin zaman rayuwa
Hakazalika, Pohamba yana son Sin da kawacen harajin kwastam na kudancin Afirka za su kafa yankin ciniki cikin 'yanci don sa kaimi ga samun bunkasuwar Sin da kudancin Afirka. Kana za a taimakawa daukacin kasashen Afirka bisa tsarin hadin gwiwar kungiyar AU. (Zainab)