in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron kolin FOCAC zai taimaka wajen kyautata hadin gwiwar abokantaka da ke tsakanin kasahen Sin da Afirka
2015-09-14 20:36:46 cri

Sakataren kwamitin kasar Sin mai kula da taron FOCAC, kana shugaban sashen kula da harkokin kasashen Afirka na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Songtian ya bayyana cewa, taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasashen Sin da Afirka wato FOCAC, wanda za a gudanar a karshen wannan shekara a kasar Afirka ta Kudu, zai kara kyautata hadin gwiwar abokantaka a tsakanin bangarorin Sin da Afirka daga dukkan fannoni.

Mista Lin wanda ya fadi haka yayin da yake zantawa da manema labaru yau Litinin ya kuma bayyana cewa, za a kyautata cinikin kayayyaki a tsakanin kasashen Sin da Afirka, zuwa cinikin sarrafa kayayyaki, yin hadin gwiwa ta fuskar kera kayayyaki, yin musayar fassaha. Kana a maimakon samun kwangilar gudanar da ayyukan gine-gine za a fi mai da hankali kan ayyukan zuba jari, tafiyar da kamfanoni, da yin hadin gwiwa ta fuskar sha'anin kudi.

Har wa yau kuma, Mista Lin ya ce, yanzu kasashen Sin da Afirka suna taimakawa juna kwarai da gaske wajen harkokin raya kasa bisa manyan tsare-tsare. Haka kuma suna bukatar juna, kuma suna da nasu fifiko yayin da suke hada kai wajen samun ci gaba. Alal misali, kasashen Afirka na da yawan albarkatun kasa, jama'a da kuma kasuwanni. Kana yawancin kasashen Afirka na kokarin gaggauta zamanintar da kasashensu da kuma raya masana'atunsu.

A nata bangare kasar Sin kuwa, tana nan tana kokarin yin kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki da kuma kyautata masana'antunta. Bugu da kari tana nuna fifiko a fannonin kudi, fasaha, kwararru, kayayyaki masu inganci da araha, da kyakkyawar kwarewa a bangaren kera kayayyaki. Abu mafi muhimanci shi ne kasar Sin tana da burin taimakawa kasashen Afirka ba tare da wata rufa-rufa ba ta yadda za su tsaya da kafafunsu. Sabili da haka ne ma kasashen Sin da Afirka suke fuskantar kyakkyawan zarafi wajen yin hadin gwiwa a tsakaninsu, wanda zai yi wuyar samuwa a tarihi. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China