in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin kaddamar da wani littafi mai taken "jimloli 500 dangane da Sin, Afirka da dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka" a jami'ar Peking ta Sin
2015-09-11 10:32:55 cri
A jiye ne aka yi bikin kaddamar da wani littafi da aka wallafa mai taken "jimloli 500 dangane da Sin, Afirka da dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka" a jami'ar Peking ta Sin, inda aka kuma kaddamar da wata gasa ta fuskar ilmi karkashin gadar sada zumunta tsakanin Sin da Afirka.

Shugaban kungiyar ma'aikatan diflomasiyya ta Sin, kana tsohon ministan harkokin wajen kasar Li Zhaoxing da kuma babban sakataren dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka, kana shugaban sashen Afirka na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Songtian sun halarci bikin tare da yin jawabai.

Li Zhaoxing ya bayyana cewa, littafin da aka kaddamar zai ba da babbar gudummawa wajen karfafa fahimtar juna da zumuncin dake tsakanin jama'ar Sin da Afirka, a sa'i daya kuma, gasar ilmi dangane da zumuncin Sin da Afirka da aka shirya karkashin Gadar sada zumunci za ta inganta mu'amalar dake tsakanin jama'ar Sin da Afirka, wadannan harkokin biyu suna da muhimmiyar ma'ana wajen ciyar da mu'amalar zumuncin dake tsakanin jama'ar kasashen biyu gaba.

Littafin mai taken "jimloli 500 dangane da Sin, Afirka da dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka" ya takaita jimloli guda 500 dangane da tarihi, yanayi, al'adu, siyasa, tattalin arziki, zaman takewar al'umma na Sin da Afirka, haka kuma, littafin yana kunshe da jimlolin dake shafar ci gaban dangantakar Sin da Afirka da kuma hadin gwiwar dake tsakaninsu, lamarin da ya sa, littafin ya kasance wata muhimmiyar kafa da za ta taimakawa jama'ar Sin da Afirka wajen kara fahimtar juna.

Shugaban sashen Afirka na ma'aikatar harkokin wajen Sin Lin Songtian ya ce, a halin yanzu, Sin da Afirka na da buri iri daya ta fuskar neman bunkasuwa. A yayin taron koli na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afirka da za a kira a kasar Afirka ta Kudu, ana fatan sanar da sabbin manufofin Sin game da yadda za ta kara inganta dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afirka domin ciyar da dangantakar abokantaka dake tsakaninsu zuwa gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China