Mataimakin ministan harkokin tuntubar juna na kasar Sin Liu Hongcai wanda ya karanta takardar kiran a bikin rufe taron, ya jaddada cewa, Sin tana son yin kokari tare da kasashen Afirka wajen inganta hadin gwiwa a tsakanin jama'ar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.
Kasar Sin ta yi kira ga kungiyoyin da ba na gwamnati ba, kafofin watsa labaru, kamfanoni da hukumomin gwamnati da sauransu da su sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, da kara fahimtar juna ta hanyar yin mu'amala, da kara yin imani da juna ta hanyar yin hadin gwiwa, da bayyana ra'ayoyin Sin da Afirka a yayin da ake yin kwaskwarima kan sabon tsarin rayuwa na duniya, da kara kyautata tsarin dandalin tattaunawa a tsakanin jama'ar Sin da na nahiyar Afirka.
Shugaban kwamitin gudanarwa na majalisar kula da harkokin tattalin arziki da zamantakewar al'umma da al'adu na kungiyar AU Joseph Chilengi ya bayyana cewa,a wannan karon dandalin tattaunawar zai mayar da hankali wajen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka. A nata bangaren majalisarsa za ta kafa wani zaunannen kwamiti mai kula da yin mu'amala a tsakanin jama'ar bangarorin biyu, da ba da muhimmanci wajen raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin. (Zainab)