Shugaban babban taron, Sam Kutesa ya bayyana a yayin bikin rufe muhawara cewa mahalartan da suka gabatar da jawabansu sun fi maida hankali kan taken wannan shekara, dake aiwatar da jadawalin cigaban bunkasuwa a shekarar 2015.
Sun jaddada muhimmancin ginawa bisa samun nasara kan da karfi muradun sabon karni na samun cigaba da kuma tsara ajandar cigaban da ake son cimma, da zai kawo alfanu mai nagarta da kuma zai kyautata zaman rayuwar kowa, in ji mista Sam tare da bayyana cewa dukkan tawagogi sun jaddada muhimmancin sanya batun kawar da talauci da yunwa a tsakiyar ajandar neman cigaba na bayan shekarar 2015.
Mista Kutesa ya nuna cewa batutuwan zaman lafiya da tsaro sun dauki muhimmin matsayi a yayin muhawara, inda yawancin masu yin jawabi suka bayyana damuwarsu kan batun barazanar kungiyoyin ta'addanci da masu tsattsarin tsattsaran kishin islama na ISIS, Al-Qaida, Al-Chabaab, Boko Harama da sauransu dake dada karuwa. (Maman Ada)