A cikin sanarwar, an ce bisa wannan tsarin dokoki na wucin gadi shugaban farar hula na kasar Burkina Faso zai iya gudanar da harkokin kasa na tsawon shekara guda yadda ya kamata. Ban Ki-moon yana fatan za a sa hannu kan tsarin dokokin, kuma shugaban farar hula na wucin gadi zai ci zabe da kuma yin rantsuwar kama aikinsa, kana hukumar wucin gadi za ta fara aiki yadda ya kamata.
Bayan haka kuma, sanarwar ta ce, Ban Ki-moon ya nuna yabo ga bangarori daban dabban na kasar ta Burkina Faso saboda kokarin da suka yi a yayin tattaunawar da aka gudana a duk fadin kasar, da kuma nauyin da suke dauka bisa wuyansu. Haka zalika Ban Ki-moon ya nuna yabo ga kokarin da MDD, da tawagar hadin kai ta AU da ECOWAS, da kuma kasashen duniya suka yi na shiga tsakani a rikicin kasar Burkina Faso. (Bilkisu)