Ziyarar shugabannin biyu ta zo ne yayin da jam'iyyun siyasar kasar da kungiyoyin fararen hula suka gabatarwa jagoran rikon kwaryar kasar Laftana kanar Isaac Zida wani daftari wanda ke kunshe da shirin mika mulki ga hannun farar hula,kafa gwamnatin rikon kwarya mai mambobi 25 da 'yan majalisun dokokin rikon kwarya guda 90.
Bugu da kari a ranar Litinin ma shugaban kasar Muaritania kana shugaban kungiyar tarayyar Afirka (AU) Mohamed Ould Abdel Aziz ya gana da dukkan bangarorin da abin ya shafa don ganin an taimakawa kasar ta Burkina Faso lalubo hanyoyin warware wannan matsala da kanta ta hanyar mika mulki ga hannun farar hula.(Ibrahim)