Shugaban kasar Sin ya aika da sako ga taron dandalin tattaunawar hakkin bil Adam da aka bude a birnin Beijing
A yau ne aka bude taron dandalin tattaunawar kare hakkin bil Adam na shekarar 2015 a nan birnin Beijing, kuma shugaban kasar Sin Mr. Xi Jinping ya aika da sako don taya murnar bude taron, inda ya jaddada cewa, burin al'ummar duniya shi ne tabbatar da kare hakkin bil Adam, don haka, ya kamata a karfafa mu'amala a tsakanin kasa da kasa ta fannonin al'adu da hakkin bil Adam, don ciyar da batun kare hakkin bil Adam na kasa da kasa gaba.
Mr. Xi ya kara da cewa, tun daga tsakiyar karni na 19 ne jama'ar kasar Sin sun fuskanci wahalhalu, wannan ya sa suka fahimci muhimmancin hakkin bil Adam da mutunta ci gaban zamantakewar al'umma, abin da ya sa suke matukar kaunar zaman lafiya, tare da nacewa ga bin hanyar samun ci gaba cikin lumana, da ciyar da harkar kare hakkin bil Adam gaba a kasar Sin da ma duniya baki daya. (Lubabatu)