Carter ya ce Amurka da Sin ba su kafa kawance a wannan fanni ba, amma kuma a hannu guda ba abokan gaba ba ne. ya ce dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin na da karfi da muhimmanci kwarai ga tsaro, da kuma wadatar dukkan duniya baki daya.
Minista Carter wanda ya kama aiki cikin watan Febrairun bana, zai ziyarci kasar Japan, da Koriya ta Kudu, a ranar 7 zuwa 10 ga wannan wata da muke ciki. Gabanin tashin sa ya yi jawabi a cibiyar nazari ta McCain dake jami'ar jihar Arizona a ranar jiya Litinin 6 ga wata.
A cikin jawabin na sa, Carter ya bayyana cewa ba zai amince tasirin da Sin ke yi a yankin Asiya da tekun Pasific ya zarce na kasar Amurka ba, kana bai yarda da cewa ba,ya na fatan bunkasuwar tattalin arzikin Sin za ta , ba zai rage damar matasa Amurkawa ba.
Carter ya kara da cewa samun nasarar Sin, ba ya nufin Amurka ta gaza. Domin akwai babbar dama ta daban a yankin na Asiya da tekun Pasific, wato batun cimma moriyar juna. Ya ce, akwai hadin gwiwa da kuma takara. Yayin da ake raya dangantaka tsakanin Sin da Amurka, kamata ya yi bangarorin biyu su kara fahimtar juna, da rage illa da ka iya samun dangankatar dake tsakanin su. Ya ce wannan ne dalilin da ya sa shugabannin kasashen biyu suka cimma yarjejeniyoyi biyu, game da fahimtar juna a bara. (Zainab)