Jami'in wanda ya bukaci a boye sunansa, ya kara da cewa kasashen biyu, za su shirya taron shawarwari game da tattalin arziki, da manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu, aikin da zai kasance wani mataki na karfafa shirin ziyarar ta shugaban Xi a Amurka.
A daya hannun kuma, babbar jami'a mai kula da harkokin Asiya, ta kwamitin tsaro a fadar ta White House Evan Medeiros, ta ce a Talatar nan shugaba Obama na Amurka, zai zanta da firaministan Japan Shinzo Abe, inda batu game da kasar Sin zai kasance daya daga jigunan tattaunawar ta su.
Madam Medeiros ta ce kasar Sin babbar kasa ce a yankin Asiya da tekun Pasific, kana kasashen Amurka da Japan na fatan tabbatar da ci gaba, da kiyaye kyakkyawar dangantakar bangarorin biyu, wadda ke da matukar amfani ga sassan.
Kaza lika kasashen biyu, na son hadin gwiwa da kasar Sin yayin da ake kula da harkokin Asiya, da na kasa da kasa, don magance kalubale a fannin tattalin arziki, da tsaro, kuma Amurka da Japan na maraba da bunkasuwar kasar Sin.(Bako)