Sanarwar ta bayyana cewa, hukumar FIFA ta gano wasu zarge-zarge da aka yiwa Valcke, kana ta bukaci kwamitinta na kula da da'ar ma'aikata da ya gudanar da bincike a kan sa.
Jérôme Valcke mai shekaru 54 da haihuwa, ya zama babban sakataren hukumar FIFA a shekarar 2007. Yayin da ake bincike kan laifuffukan cin hanci a hukumar ta FIFA, an zarge shi da fidda kudi har dala miliyan 10 daga kasar Afirka ta Kudu, zuwa aljihun Jack Warner a shekarar 2008, wanda a lokacin ke kan kujerar shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta yankin Arewacin Amurka da ta tsakiya, da yankin Caribbean .
A ganin hukumar shari'a ta kasar Amurka, fidda wadannan kudi a matsayin toshiyar baki, yana da nasaba da neman baiwa kasar Afirka ta Kudun damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya da ya gabata a shekarar 2010. (Zainab)