in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Blatter ya sake zama shugaban FIFA
2015-05-30 16:50:29 cri

Ranar 29 ga wata, Sepp Blatter ya sake zama shugaban kungiyar wasan kwallon kafa ta kasa da kasa wato FIFA, a lokacin da ake zargin hukumar kwallon kafa ta duniya da laifin cin hanci da karbar rashawa.

Shugaban na yanzu ya lashe mataimakinsa Yarima Ali bin al-Hussein na kasar Jordan ne a cikin zaben da kungiyar ta gudanar a birnin Zurich na kasar Switzerland. Wannan shi ne karo na 5 a jere da mista Blatter mai shekaru 79 a duniya yake zama shugaban kungiyar.

A cikin gajeren jawabinsa bayan ya ci zaben, mista Blatter ya gode wa goyon baya da sassa daban daban suka nuna masa. Ya kuma bayyana cewa, zai sauke nauyin ba da jagoranci wajen dawo da martabar kungiyar ta FIFA. Ya lashi takobin cewa, surar kungiyar FIFA za ta samu kyautatuwa kafin ya kammala wa'adin aikinsa a wannan karo.

Bayan barkewar abun kunya mafi tsanani da kungiyar FIFA ta taba fuskanta a tarihinta, wato ana tuhumar manyan jami'anta da cin hanci da rashawa, mista Blatter ya fuskanci babban matsin lamba daga mambobin kungiyar, manyan kamfannonin ba da taimako, wadanda suka bukace shi dakatar da zaben, har ma sun tilasta masa yin murabus. Kafin wannan kuma Michel Platini, shugaban kungiyar wasan kwallon kafa ta nahiyar Turai ya bayyana cewa, yawancin mambobin kungiyarsa za su mara wa Yarima Ali bin al-Hussein baya a lokacin kada kuri'a.

Amma ana ganin cewa, kuri'un amincewa da mambobin kungiyar FIFA wadanda suka fito daga kasashen Afirka, Asiya, arewaci da tsakiyar nahiyar Amurka, da yankin Caribbean suka jefa sun taka muhimmiyar rawa a cikin zaben. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China