Rahotanni na nuna cewa, yayin taron an tattauna batutuwan dake shafar yankunan da aka tura sojojin, yawan sojojin da aka jibge, ka'idojin gudanar da ayyuka, jadawalin ayyukan da za su gudanar, yawan kudin da za a kashe yayin da ake gudanar da ayyuka da dai sauransu. An tabbatar da cewa, yawan sojojin hadin gwiwar ya kai 8700, kuma za a raba su ne a rukunoni 5, inda za a jibge su a yankuna 3 na yakin. Kana an kafa hedkwatar da ke kula da rundunar sojojin a birnin N'Djamena na kasar Chadi. (Zainab)