Bam din farko dai an ce ya fashe ne a tsakiyar kasuwa a garin Kerawa wanda yake kan iyaka da kasar Nigeriya sannan bam na biyu ya fashe a kusa da wani sansanin soji inda a nan ne mutane 15 suka mutu kamar yadda wata majiyar tsaro ta tabbatar.
Wadanda suka mutu dai a kasuwa har yanzu ba'a samu adadin su ba, in ji majiyar da ta nemi a sakaya sunanta.
Kasar Kamaru dai ta shiga cikin jerin kasashe na hadin kan yankuna na Afrika da ke yaki da kungiyar 'yan Boko Haram na Nigeriya. Garin Kerawa dai yana da nisa daga arewacin kasar, kuma ya fuskanci gwagwarmaya tsakanin sojin kasar da na 'yan kungiyar Boko Haram. (Fatimah Jibril)