in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: A kalla mutane 26 aka kashe sakamakon kare haren Boko Haram
2015-09-03 10:31:01 cri
A kalla mutane 26 suka mutu a cikin wasu hare-haren da ake zargin mayakan Boko Haram da kaiwa a kauyuka biyu na jihar Borno, dake arewa maso gabashin Najeriya, a cewar wani mazaunin wurin a ranar Laraba.

A ranar Litinin da yamma, mayakan sun kai farmaki a kauyukan Kolori da Ba'ana Imam, in ji Mamman Usman, mamban na wata kungiyar wurin.

Boko Haram ta shiga Kolori a kan dawaki sannan suka fara harbin mutane da bindigogi, in ji Usman dake rawaito kalaman wasu mutanen da suka tsirar da rayukansu a lokacin harin, mutane 18 aka kashe a Kolori.

Haka kuma, maharan sun kona gidajen jama'a tare da yin awon gaba da abinci da dabbobi.

Wani mutumin da ya tsirar da rayuwarsa mai suna Mohammed Ali, ya bayyana cewa mutanen da suka ji karamin rauni an kai su wani sansanin 'yan gudun hijira domin samun jinya.

A jajibirin wadannan hare-hare, sojojin Najeriya sun karbe muhimmin birnin Gamboru Ngala dake jihar Borno daga hannun mayakan Boko Haram. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China