in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Luis Enrique na hasashen nasara ga Barca duk da rashin nasarar da ya kwasa a hannun Man Utd
2015-07-30 09:51:07 cri
Kocin Barcelona Luis Enrique ya ce kulaf din sa na da cikakkiyar dama, ta cimma manyan nasarori, duk da doke su da Manchester United ta yi da ci 3 da 1 a birnin San Francisco, a wasan share fagen shiga kakar wasanni mai zuwa.

Enrique ya ce rashin sa'a ne kawai ya sanya Manchester basu ruwa, kuma duk da wannan rashin nasara da suka samu ya yi amannar cewa 'yan wasan sa sun yi iyakacin ikon su.

"bamu yi wasa irin wanda ake fatan gani ba, amma babu damuwa, domin kuwa muna da lokaci tun daga nan zuwa 11 ga watan Agusta, na gudanar da gyare-gyare" a kalaman koci Enrique.

Kaza lika kocin na Barcelona ya bayyana karawar da suka yi da manyan kulaflika a baya bayan nan, a matsayin wata hanya ta kimtsawa, yana mai cewa nan gaba kadan za su fara buga gasar zakarun turai, da kuma ta kofin kalubale na Sifaniya. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China