Da yake karin haske game da hakan, shugaban kungiyar ta Madrid Florentino Perez, ya ce kasancewar Real Madrid kulaf mafi kwarewa a duniya, alakar sa da kamfanin Alibaba za ta bada damar bunkasa harkokin kasuwancin kulaf din a kasar Sin.
Real Madrid, wanda ya dauki kofin zakarun turai har karo 10, zai zamo na biyu bayan kulaf din Munich na Jamus, wanda ya shiga hada-hadar cinikayya da kamfanin na Alibaba. Karkashin yarjejeniyar shagon Tmall.HK zai rika sayar da takalma, da kayan sawa na kwallon kafa masu dauke da tambarin kungiyar ta Real Madrid.
A nasa bangare wakilin kamfanin na Alibaba Zhang Jianfeng, ya ce yana fatan wannan sabon tsari zai baiwa kamfanin sa cikakkiyar damar sayar da hajojin Real Madrid a nan kasar Sin. (Saminu Alhassan)