Kungiyar cibiyoyin kudin cigaban Afrika a ranar Talata suka amince su tsara wani shiri da zai kawo karin jari da kuma hanyoyin da za'a samu dabarun samar da kudi a bangaren tattalin arziki.
Wannan amincewa dai, an cimma shi ne a wajen babban taro karo na 49 na bankin raya kasashen Afrika ADB da yanzu haka ake yin shi a Kigali, babban birnin kasar Rwanda.
Da yake jawabi a lokacin taron na yini 5 mai taken "Shekaru 50 masu zuwa, Afrikan da muke bukata", shaihun malami Samuel Wangwe, wani mai nazari a harkokin tsare-tsare a Tanzaniya ya ce, hanya mafi dacewa da za'a bi a magance talauci, sannan a cigaba da tabbatar da hauhawar tattalin arziki ita ce a kara yawan abubuwan da ake bukata, sannan a samar da guraben ayyukan yi. (Fatimah)