in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afrika sun amince da ajandar yaki da talauci bayan 2015
2014-06-26 11:00:41 cri

shugabar kasar Liberia Ellen Shirleaf Johnson, ta ce, kasashen Afrika sun dauki alkawari na kaddamar da shawarwari dake cikin yarjejeniyar nahiyar ta Afrika domin ganin an samu nasarar kaddamar da ajandar ci gaba bayan shekara ta 2015.

A yayin da take jawabi ga wani taron koli na shugabannin kasashen Afrika a Malabo dake Equatorial Guinea, shugabar kasar Liberia, kana kuma shugabar kwamitin raya kasa bayan shekara ta 2015, ta ce, tun bayan da kasashen Afrika suka samu murya guda a game da maganar ajandar bayan shekara ta 2015, an samu nasarar gudanar da abubuwa da yawa domin zaburar da cikakken ci gaba mai inganta jin dadin rayuwa da kuma la'akari da muhalli.

Shirleaf Johnson ta lura da cewar, a karon farko, kasashen Afrika sun sami damar zayyana sabuwar makoma a game da ci gaba mai dorewa, tare da zaman lafiya da kwanciyar hankali. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China