Cikin wasikar da Matteo RENZI, firaministan kasar Italiya ya rubutawa manyan kafofin watsa labarai na kasashen Turai a kwanakin baya, ya ce kasashen yamma sun kasa hangen mummunan tasirin da shirye-shiryen da suka tsarawa kasashen Libya, da Syria za su haifar a gaba, haka kuma sun yi kuskure wajen ganin kansu a matsayin masu karfin kafa sabbin hukumomi a kasashen 2.
Shi kuwa tsohon ministan harkokin wajen kasar Italiya, Franco Frattini, cewa ya yi rashin hangen nesa ne ya sa kasashen yammacin duniya suka aikata babban laifi a kasar ta Libya, inda janyewar sojojinsu ta haifar wa kasar tsunduma cikin babbar matsala. Zuwa yanzu dakarun kasar Libya suna kokarin hada baki da masu tsattsauran ra'ayi na kungiyar IS, lamarin da ya haddasa yakin basasa a kasar, gami da barazanar tsaro ga kasashen Turai.(Bello Wang)