A cikin sanarwar da ma'aikatar kula da harkokin wajen kasar Faransa ta bayar, an ce, wadannan kasashe uku na sa ran shiga cikin jerin kasashen da za a kafa bankin AIIB, tare da inganta hadin gwiwa da kasashen duniya, don dukufa ka'in da na'in wajen kafa wata hukumar da za a tabbatar da ingancin samar da rance da manyan ayyukan more rayuwa.
A cikin sanarwar, an ce, bankin AIIB zai taka muhimmiyar rawa game da raya manyan ababen more rayuwa a kasashen Asiya, tare da ba da babbar gudummawa wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma a shiyya-shiyya da ma kasashen duniya baki daya.
A wannan rana, yayin da kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Hong Lei yake bayani ga manema labaru, ya ce, bankin AIIB wata hukumar samar da bunkasuwa ce da ke kunshe da fannoni da dama, don haka Sin tana maraba da kasashen da ke da niyyar shiga cikin bankin da su gaggauta yanke shawara don zama kasashe da za su kafa hukumar.
Ya kuma kara da cewa, shigar da kasashen Asiya da sauran kasashe cikin hukumar, zai yi amfani sosai wajen shaida wakilcin bangarori da dama a hukumar.
Kasar Sin ta yi tayin kafa bankin AIIB wajen raya manyan ababen more rayuwa a Asiya,kuma za a kafa cibiyarta a birnin Beijing fadar gwamnatin kasar.(Bako)