in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da musulmai 2800 dake yankin Ningxia na Sin ne suka tafi aikin hajin bana
2014-09-05 16:07:24 cri
A yau Jumma'a 5 ga wata ne, jirgin sama na farko dake dauke da musulmai guda 297 daga yankin Ningxia mai cin gashin kansa na kasar Sin ya tashi daga filin jirgin sama na Yinchuan zuwa birnin Makka, inda za su yi aikin haji. A wannan shekara, gaba daya musulmai guda 2833 a yankin na Ningxia za su tafi birnin Makka don yin aikin haji bisa taimakon gwamantin kasa ta Sin, adadin da ya kasance mafi yawa cikin shekaru da dama da suka gabata.

Kuma musulman da suka tafi birnin Makka a yau ita ce tawaga ta farko daga yankin Ningxia da ta tashi zuwa birnin na Makka.

Dimin samar da sauki ga mahajjatan, ban da ma'aikata, akwai kuma likitoci, masu dafa abinci a cikin tawagar da ta tashi zuwa birnin na Makka a yau, wadanda dukkansu gwamantin kasar Sin ta tanada musu.

Yankin Ningxia na kabilar Hui mai cin gashin kansa, yana daya daga cikin yankuna masu cin gashin kansa na kananan kabilu guda biyar na kasar Sin, inda yawan mazaunan wurin 'yan kabular Hui dake bin addini musulunci ya kai kimanin miliyan biyu da dubu 326. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China