A ran 13 ga wata, hanyar jiragen kasa da ke a birnin Makka, wadda kamfanin gine-ginen hanyar jiragen kasa na kasar Sin CRCC ya gina, ta yi aikin jigilar maniyyata masu yawan gaske da suka zo birnin Makka mai tsarki na addinin Musulunci da ke kasar Saudiya. Wannan ya zama shekara ta hudu a jere da kamfanin CRCC ya bayar da hidimar jigilar maniyyata na kasashe daban daban na duniya.
An yi hasashen cewa, a wannan shekarar da muke ciki, za a yi jigilar maniyyata kimanin miliyan 2 da dubu 500 a cikin kwanaki 5.
Kamfanin CRCC ya fara gina hanyar dogo a Makka ne daga shekara ta 2009, kuma an fara yin amfani da ita a hukunce a watan Nuwamba na shekara ta 2010, wadda tsawonta ya kai kilomita 18.25, kuma tana da tashoshi 9, wadanda suke kaiwa da kawowa tsakanin yankuna 3 da ake yin aikin hajin, wannan ya sa, hanyar dogon ta kawo sauki ga maniyyata daga sassa daban daban na duniya ta yadda za su yi aikin haji lami lafiya kuma da sauri, sakamakon haka hanyar dogo da kamfanin kasar Sin ya gina ta samu yabo sosai daga kasashen musulmai.(Danaldi)