Rahotanni daga birnin Makka na kasar Saudi Arabiyya ya ce, wadanda suka mutu ya zuwa yanzu sakamakon hadarin fadowar karfen daukan kaya a masallacin Harami sun kai 107 sannan wassu 238 sun ji rauni kamar yadda gidan talabijin din birnin na Makka ya sanar a ranar Jumma'a.
Talabijin din Al-Arabiya tun da farko ya ce, karfen daukan kayan ya fado ne sabo da tsawa da aka yi mai karfi, abin da kasar take fuskanta a 'yan kwanakin nan.
Mahukuntar kasar tuni ta kaddamar da bincike kan lamarin, sannan an samar da ma'aikatan kare jama'a da bada agaji na jiyya a wajen da hadarin ya faru. Haka kuma dukkanin asibitoci na birnin Makka suna cikin shiri na karbar karin wadanda suka samu rauni.
Wannan karfen daukan kayan dai ya fado ne saboda rashin kyaun yanayi kuma ana aiki da shi ne a ayyukan fadada masallacin Haramin da ake yi.
Hadarin da ya faru lokacin da kasar ta fara karbar maniyya aikin hajjin bana daga dukkan fadin duniya da za'a fara nan da 'yan kwanaki, bayan kammala aikin fadada haramin da ake yi a yanzu wanda shi ne mataki na karshe, ana sa ran masallacin zai dauki fiye da mahajjata miliyan 3 a cikin awa daya.
Fadada masallacin da ake yi nada zummar daukar karin maniyyata dake zuwa ibada ne daga duk fadin duniya musamman lokacin aikin Haji.(Fatimah Jibril)