Kasar Benin ta bayyana goyon bayanta ta hanyar aike da wata rundunar sojoji dake kunshe da mutane 800 a kusan takwarorinsu na Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi, a karkashin rundunar hadin gwiwa da za ta fara ayyukanta nan da 'yan kwanaki masu zuwa domin ganin an kawo karshen kungiyar Boko Haram baki daya.
Haka kuma wannan majiya ta nuna cewa, shugaba Boni Yayi zai yi shawarwari tare da gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, kan batun cigaban dangantakar kusanci tsakanin Benin da jihohin tarayyar Najeriya.
Dangantaka tsakanin Benin da Najeriya na dogaro kan wasu takardun doka goma, wadanda suka hada da dangantakar taimakon juna, zuwa yarjejenoyin dangantakar tattalin arziki, kimiyya da fasaha. (Maman Ada)