Rahotanni daga Najeriya na cewa, an bankado wasu mayakan Boko Haram guda 22 cikin 'yan Najeriya 12,000 da aka tuso keyarsu daga kasar Kamaru da a halin yanzu aka tsugunar da su a sansanin Mubi da ke jihar Adamawa.
Babban darektan hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) Muhammad Sani Sidi, ya shaidawa manema labarai a Abuja, fadar mulkin kasar cewa, a damke 'ya'yan kungiyar ce a kokarin da suke na kaddamar da hare-hare. An kuma bankado su ne ta hanyar gano wasu alamu da aka yi musu a bayan su, abin da ke nuna cewa, sun yi shahada.
Yanzu haka dai akwai sansanonin tsugunar da mutanen da suka gudu daga muhallansu sakamakon hare-haren Boko Haram har guda 23 a jihar Borno. Kuma gwamnatin jihar na shirin kara bude wasu sakamakon karuwar mutanen da bala'in Boko Haram ke raba su da muhallansu a ko wace rana.
Mayakan Boko Haram dai sun kara zafafa kai hare-haren bama-baman kunar bakin wake da sauran hare-hare a sassa daban-daban na jihohin Borno, Yobe da kuma jihar Adamawa dake arewa maso gabashin kasar, da kuma kasashen Kamaru da Chadi da Nijar da ke makwabtaka da Najeriya.(Ibrahim)