in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya na kai hare hare ta sama kan sansanonin Boko Haram da ke dajin Sambisa
2015-08-20 10:26:00 cri

Sojojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram da dama da ke tserewa daga dajin Sambisa bisa ga lugudan wuta ta sama da rundunar sojojin Najeriya take ci gaba da kai wa, in ji wani jami'in soja a ranar Laraba.

Kakakin rundunar sojojin Najeriya, Kanal Sani Kukasheka Usman, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, dakarun Najeriya sun shiga yankin arewa maso gabashin kasar, inda kuma suka tafka kazamin fada tare da mayakan kungiyar Boko Haram.

Tare da bayyana cewa 'yan ta'addan na tserewa daga dajin Sambisa, sojojin Najeriya dauke da makamai na zamani, sun samu nasarar kashe mayakan Boko Haram da dama.

Kanal Kukasheka Usman ya kara da cewa, sojoji kuma sun lalata motoci, babura da makaman kungiyar. Haka kuma sojoji na ci gaba da yin sintiri da kai samame kan 'yan ta'adda a wannan yanki.

Har ila yau, rundunar sojojin saman Najeriya ta bayyana yawaita kai hare hare ta sama kan mayakan Boko Haram da ke dajin Sambisa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China