in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An jinjinawa jawabin firaministan Sin dangane da tattalin arzikin kasar
2015-09-11 14:36:07 cri
An bude taron dandalin tattalin arziki na Davos na lokacin zafi na bana a ranar Alhamis, taron da ke gudana a birnin Dalian dake arewa maso gabashin kasar Sin.

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya halarci bikin bude taron tare da gabatar da jawabi kan yanayin tattalin arzikin kasar Sin. A cewarsa tattalin arzikin kasar Sin ba ya kan hanyar gurguncewa, kuma kasar ba za ta aiwatar da gyaran fuska ga darajar kudin ta na RMB don samun damar fitar da karin kayayyaki zuwa ketare ba. Haka kuma ya ce wasu kamfanonin kasar Sin suna kokarin habaka harkokinsu zuwa kasuwanni daban daban, inda wadannan kamfanonin suke taka muhimmiyar rawa ta fuskar raya tattalin arzikin Sin.

Jawabin da firaministan ya yi ya karfafa gwiwar masu zuba jari na kasashen waje, ta hanyar nuna musu niyyar gwamnatin kasar Sin ta kyautata tsarin tattalin arziki, da kiyaye karuwarsa cikin sauri, gami da kokarin samun ci gaba.

A cewar mista Qin Hongtao, shugaban kamfanin Heng Chang mai kula da harkar zuba jari a fannin hada-hadar kudi na birnin Beijing, maganar faraministan ta sanya kamfanonin dake kokarin kirkiro sabbin fasahohi samu kwarin gwiwa matuka.

"Kamfaninmu na kula da hada-hadar kudi ta hanyar yanar gizo ta Internet. Ma iya cewa, bayan da na ji maganar firaminista, na samu kwarin gwiwa sosai. Na yarda da manufar da gwamnatinmu ta gabatar ta sanya jama'a da yawa su shiga a dama da su a fannonin kirkiro sabbin fasahohi, gami da bude sabbin kamfanoni masu zaman kansu. A nan gaba za mu bi manufar sau da kafa don samun karin damammakin bunkasa sha'aninmu."

A nasa bangare, Zhu Min, mataimakin babban darektan asusun ba da lamuni na IMF, ya ce kirkiro sabbin fasahohi na taimakawa tattalin arzikin duniya wajen samun ci gaba.

"A bisa yanayi na samun jama'a da yawa da suke shiga aikin kirkiro sabbin fasahohi, ina ganin cewa gwamnatin kasar Sin za ta samu damar kyautata tsarin tattalin arzikin ta daga tushe, idan ta iya sanya jama'arta maida hankali kan raya masana'antu, da aikin fitar da kayayyaki."

A cikin jawabinsa, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana yanayin da tattalin arzikin kasar Sin yake ciki na "hawa da sauka, amma tare da kasancewa cikin kyakkyawar makoma", inda ya ce sana'o'i masu alaka da cigaban fasahohi na samun bunkasuwa cikin sauri, yayin da ayyukan tsimin makamashi da kiyaye muhalli su ma ke tasowa, saboda haka ana samun fannonin da za su tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasar a nan gaba. Firaministan ya nanata cewa, tattalin arzikin Sin zai dinga samun ci gaba, kuma hakan ba wai kwarin gwiwa ne maras dalili ba, domin akwai tushen raya tattalin arzikin, kuma akwai sharuddan da suke taimakawa samun ci gaba.

Bayan da ya saurari jawabin firaministan kasar Sin, Fahmy Tarazi, wani shehun malami daga jami'ar Harvard ta kasar Amurka, ya ce jawabin ya zamo damar isar da sakonni masu ma'ana kan yanayin tattalin arzikin kasar ta Sin,

"Jawabin da ya yi, ya karfafa wa masu zuba jari gwiwarsu kan yanayin tattalin arzikin kasar Sin, da makomarsa a nan gaba, don haka zai taimakawa, wajen kau da fargaba da shakku da aka samu a tsakanin masu ruwa da tsaki a cikin kasuwannin kasa da kasa. Firaministan ya bayyana karfin tattalin arzikin Sin, kuma ya ambaci kalubalen da ake fuskanta, amma ya ce gwamnatin kasar Sin tana da imani kan warware wadannan matsaloli."

Mista Fahmy Tarazi ya kara da cewa, hanyar da ta zama dole a bi ita ce kokarin bude sabbin sana'o'i, gami da hada su da kasuwannin kasashen waje. Ta la'akari da wannan yanayin da ake ciki ne, ya dace kasar Sin ta ci gaba da kokarinta na kwaskwarimar tsarin tattalin arzikinta. Manufar a cewar mista Fahmy za ta yi amfani, kuma ana sa ran ganin karin amfanin ta a nan gaba. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China