in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta sake tsara shirin yin hadin gwiwa tsakaninta da sauran kasashen duniya a fannin samar da kayayyaki da kuma kera na'urori
2015-05-07 15:58:41 cri

A jiya ne majalisar gudanarwar kasar Sin ta kira wani taro, inda ta tsaida kudurin sake sa kaimi ga shirin yin hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya a fannin samar da kayayyaki da kuma kera na'urori,ta yadda za ta sa kaimi ga samun bunkasuwa ta hanyar fadada fannonin shirinta na bude kofa. Wannan ne karo na biyu a bana da majalisar gudanarwar kasar Sin ta tsara aikin yin hadin gwiwa a tsakaninta da sauran kasashen duniya a wannan fanni.

Firaministan kasar Sin Li Keqiang shi ne ya shugabanci taron majalisar gudanarwar kasar Sin da aka kira a jiya Laraba 6 ga wata, inda aka tsara aikin yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da sauran kasashen duniya a fannin samar da kayayyaki da kera na'urori don sa kaimi ga samun bunkasuwa ta hanyar fadada fannonin shirin kasar na bude kofa ga kasashen waje. Ana ganin cewa, wannan shiri zai taimaka wajen hade hada tattalin arzikin Sin da na duniya waje guda, da sa kaimi ga farfado dawar tattalin arzikin duniya, har ma za a sa kaimi ga kamfanonin Sin da su inganta aikinsu tare da samar da kayayyaki masu inganci, wannan zai taimaka wajen inganta tsarin tattalin arziki da shirin bude kofa na kasar Sin da kuma samun tabbatar da moriyar juna da bunkasuwa tare tsakanin kasashe daban daban.

Kafin haka, aA gun taron majalisar gudanarwa ta kasar da aka kira a ranar 28 ga watan Janairu na bana kuwa, an tsara wani shirin yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da sauran kasashen duniya wajen fitar da kayayyakin jiragen kasa, da na'urorin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashin nukiliya, da sauran na'urorin da kasar Sin ta kera zuwa kasashen waje. Dangane da shirye-shiryen da aka tsara, wWani manazarci na cibiyar nazarin tattalin arzikin kasashen waje na kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Zhang Jianping yana ganin cewa, yayin da tattalin arzikin Sin ya shiga wani sabon tsarin yanayi na yau da kullum, kuma yayin da kasar ke kokarin aiwatar datsara shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar Siliki ta ruwa na karni na 21 wato "Ziri daya da hanya daya", aikin da ake yi na fitar da na'urorin kirar kasar Sin zuwa kasashen waje zai agazawa tattalin arzikin ta Sin da kuma na duniya gaba daya. Zhang ya bayyana cewa,

"Yanzu abin bukata shi neBurin kasar Sin na yanzu shi ne ta kyautata tsarin tattalin arzikinta, ta da kuma canja hanyar samun bunkasuwa, domin ana bukatarlamarin da ya sa ake bukatar yin amfani da aikin fitar da na'urorin kirar kasar Sin zuwa kasashen waje don fadada kasuwanni da neman sabbin fannonin samun bunkasuwa."

A gun taron, an bukaci dora muhimmanci kan fannonin sana'o'in da suke da fifikofasahar kasar Sin ke kan gaba a duniya, kamarsu shimfida layin dogo jiragen kasa, samar da wutar lantarki, sadarwa, injiniyoyi da dai sauransu, da sa'an nan a sa kaimi ga fitar da su zuwa yankunan da suke bukatar suda bukata, musamman ma domin biyan bukatun kasashen dake bin manufar shirin "Ziri daya da hanya daya" ya shafa, da sa kaimi gata yadda kasashen a nasu bangaren zada su kara samar dasamu karin guraben aikin yi, gami da damar bunkasa tattalin arzikinsu. Dangane da shawarar da aka gabatar a wajen taron, Manazarci wani masani a kamfanin hada-hadar hannayen jari na Yinhe na kasar Sin Meng Jing ya yi nazari cewa,

"Sin tana da cikakken jari da kuma karfin samar da kayayyaki masu inganci da kera na'urori, don haka aikin hada wadannan bangarori tarefannin samar da kayayyaki da kera na'urori zai samar da moriya ga kasashen dake bin manufarshirin 'Ziri daya da hanya daya' ya shafa."

Kafin wannan taro, wasu kamfanonin Sin sun dakatar dariga sun fara kokarin shiga tsarin fitar da na'urorin Sin zuwa kasashen waje. Alal misali, kamfanonin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashin nukiliya na kasar Sin suna yin kokarin fitar da injin "Hualong mai lamba 1" dake da ikon mallakar fasaha na Sinwanda kasar Sin ke da ikon mallakar fasahohinsa zuwa kasar Pakistan da sauran kasashen duniya daban daban. A nasa bangare, sShugaban kamfanin kera jiragen kasa na CSR na kasar Sin Zheng Hongchang ya bayyanawa 'yan jarida cewa, kamfaninsa yana kokarin gaggauta fitar da na'urorinsa zuwa kasashen waje. Ya ce,  

"Daya daga cikin manyan manufofin 'Ziri daya da hanya daya' shi ne gina ayyukan more rayuwa, don haka kamfaninmu na CSR yana kiyaye dangantakarkokarin ciniki tare da kasashe da dama dake bin wannan manufa tada shirin 'Ziri daya da hanya daya' ya shafa, kana ana kokarin fitar da kayayyakin jiragen kasa masu sauri zuwa kasashen waje". (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China