150703-Firaministan-kasar-Sin-ya-gabatar-da-jawabi-a-yayin-bikin-rufe-taron-koli-na-masanaantu-da-cinikayya-na-Sin-da-Faransa-Sanusi.m4a
|
A yayin bikin rufe taron, Li Keqiang ya bayyana cewa, ba ma kawai hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Faransa za ta amfana wa kasashen biyu ba, har ma za ta kasance mai fa'ida ga duniya baki daya. Li Keqiang ya ce, "Yanzu haka muna hadin gwiwa a fannonin masana'antu da makamashi, da taya kasuwanni ta bangare uku da kuma ingiza yin hadin gwiwa a fannonin masana'antu da makamashi tsakanin kasa da kasa, sannan mun yi hadin gwiwa a fannin yin amfani da makamashin nukiliya da zirga-zirgar jiragen sama da kumbon 'yan sama jannati da dai makamatansu. Irin wadannan hadin gwiwa sun bayyana cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Faransa tana da muhimmanci kwarai."
A cikin jawabinsa na karshe, Mr. Li Keqiang ya siffanta dangantakar da ke tsakanin Sin da Faransa tamkar wani jirgin sama.