in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jawabin da firaministan kasar Sin ya yi a dandalin Davos ya kawar da damuwar kasashen waje kan tattalin arzikin Sin
2015-01-23 16:48:30 cri

A cikin jawabin da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi a taron shekara-shekara na dandalin tattalin arzikin kasa da kasa na Davos, ya sanar da sabbin bayanai game da yadda aka ake kyautata tsarin tattalin arzikin na kasar Sin, wadanda suka jawo hankulan 'yan kasuwa da masana a fannin tattalin arziki na Sin da kasashen ketare. A ganin masanan kasar Sin dake halartar taron, alama sako mai kyau da firaminista Li ya nuna ta kawar da damuwar da kasashen ketare ke da shi kan tattalin arzikin Sin.

An samu saurin karuwar tattalin arziki a nan kasar Sin a 'yan shekarun da suka wuce, wannan ya sa wasu mutane ke nuna damuwa da sassaucin karuwar tattalin arzikin Sin a shekarun baya na gaba. Game da hakan, firaminista Li ya nuna alamaisar da sako mai kyau a cikin jawabinsa, inda ya ce, karuwar tattalin arzikin na kasar ta Sin ba za ta ragu cikin sauri ba, kuma kasar na kokarin daukar matakan fuskantar hadarin kudi. A ganin Li Daokui, shehun malami a sashen nazarin tattalin arziki na jami'ar Tsinhua, alkawarin da firaminista Li ya yi ya kawar da damuwar da kasashen ketare ka ke da shi kan tattalin arzikin kasar Sin.

A cikin jawabinsa, firaminista Li ya yi bayani kan manufar kyautata tsarin tattalin arzikin kasar Sin, wato saurin ci gabansa ya dan ragu zuwa matsakaicin matsayi, yayin da ingancin tattalin arzikin a daya bangare ke samun ci gaba.Shi ma shehun malami a sashen nazarin bunkasuwar kasa na jami'ar Beijing Li Yifu ya ce, wannan shi ne hakikanin halin da ake ciki bayan da kasar Sin ta shiga wani sabon matsayi.

"A cikin shekaru 36 da suka wuce, matsakaicin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya kai kashi 9.7 cikin dari a ko wace shekara, amma yanzu karuwar kimanin kashi 7 cikin dari ne, wato an samu raguwar kashi 20 zuwa 30 cikin dari ke nan. A cikin shekaru biyar da suka wuce, an kyautata tsarin tattalin arzikin kasar lamarin da ya sanya raguwar saurin bunkasuwar tattalin arziki sannu a hankali."

Shi ma shehun malami Li Daokui yana ganin cewa, idan kasar Sin na fatan tabbatar da samun karuwar tattalin arzikinta zuwa wani babban matsayi, to a yayin da take kokarin hana raguwar sa cikin sauri, a sa'I i guda bai kamata ta so karuwar tattalin arziki cikin sauri ba. Ban da wannan kuma, Li Daokui ya tabo wani misalin da firaminista Li ya bayar a cikin jawabinsa:

"Firaminista Li ya ba da wani misali da wasan zamiyar kankara, inda ya ce, garin Davos wuri ne mai ni'ima da ya dace da wasan zamiyar kankara. Da farko wasan na bukatar saurin da ya dace, idan aka yi hankali sosai, to za a zame. Na biyu ya kamata a tabbatar da daidaituwa yayin da ake zamiyar kankara. Na uku, ana bukatar kwarin gwiwa. Wadannan matakai guda uku muhimman abubuwa ne da ake bukata wajen warware matsalar tattalin arzikin kasar Sin."

Game da batun tsarin aikin masana'antu ma, a cikin shekaru 30 da suka wuce, yawancin masana'antun kasar Sin sun kasance irin wadanda ke bukatar tarin ma'aikata, wadanda ke samar da kayayyaki marasa inganci daraja sosai. Amma, saboda yawan kudaden da ake kashewa wajen biyan ma'aikata ya zama dole a canja tsarin kara samar da kayayyaki masu inganci. Shehun malami Li Yifu ya ce,

"Ko shakka babu, idan muna son canja hanyar ta muka saba yin amfani da ita a baya ta yin amfani da ma'aikata da dama, da shigo da fasahohi, zuwa sabuwar hanyar yin kirkire-kirkire bisa karfin kanmu, akwai bukatar canja tsarin da muka saba amfani da shi zuwa fannoni daban daban, ciki har da rage matakan masu sarkakiya da gwamnati ke bullo da su wajen kafa masana'antu, da neman tallafin kudi, da kuma kara zuba jari a bangaren ilmi da gwamnati za ta yi, kana da neman goyon baya daga gwamnati a fannin nazarin kimiyya."

Kan makomar tattalin arzikin kasar Sin a nan gaba, shehun malami Lin Yifu yana cike da imani cewa, a matsayinta na matsakaiciyar kasa mai matsakaicin kudin shiga, kasar Sin na da makoma mai kyau a fannin fasahar kirkire-kirkire, da inganta matsayin masana'antu, da kuma kara kyautata muhimman kayayyakin more rayuwa. Ban da wannan kuma, yawan kudin da al'ummar kasar ke ajiyewa a bankuna ya kai kashi 50 cikin dari, kana kudaden musanya da aka ajiye sun kai RMB biliyan 4000, wadannan da ma wasu sun kasance kyawawan muhalli na wajen zuba jari. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China