in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron DAVOS na shekarar 2014 a nan kasar Sin
2014-09-11 16:51:49 cri

A jiya Laraba 10 ga watan nan ne aka bude taron dandalin tattaunawa game da tattalin arziki na duniya wato DAVOS, na yanayin zafi na bana a birnin Tianjin na nan kasar Sin.

A cikin jawabin da ya gabatar yayin bikin bude taron, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jaddada cewa, kasarsa za ta ci gaba da kokarin inganta aikin kirkire-kirkire a fannonin tsare-tsare da fasahohi, da nufin daga matsayin tattalin arzikinta zuwa wani sabon matsayi.

A wannan yanayin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar kalubaloli da dama, dandalin DAVOS na bana ya janyo hankulan sassa daban daban. Wannan dandali na tattaunawa wanda ke dora muhimmanci kan inganta aikin kirkire-kirkire, da samar da daraja, ya samu halartar shugabanni sama da 1600 daga fannonin kasuwanci, da siyasa, da nazarin ilimi, da kuma 'yan jarida fiye da 500 na ciki da na waje, adadin da ba a taba ganin irinsa a tarihin dandalin tattaunawar ba.

Cikin jawabin nasa, firaminista Li Keqiang ya kara da cewa, aikin kirkire-kirkire na da ma'ana kwarai ga kasar Sin da ma dukkanin duniya baki daya.

"Ana bukatar kirkire-kirkire domin farfado da tattalin arzikin duniya, kuma kasar Sin ma na dogara da kirkire-kirkire wajen karfafa ingancin tattalin arzikinta. Sakamakon tsayawa tsayin daka kan ayyukan gyare-gyare, da na kirkire-kirkire ne, kasar Sin ta kai ga samun dauwamammen ci gaban tattalin arziki yadda ya kamata a 'yan shekarun da suka gabata."

Firaminista Li ya kara da cewa, dukkanin nasarar da kasar Sin ta samu ta fuskar tattalin arziki, na dogaro da aiwatar da kirkire-kirkire. A kuma nan gaba Sin za ta kara mayar da hankali kan kirkire-kirkiren tsarukan tattalin arziki.

To amma ko ta yaya za a kai ga cimma hakan? Firaminista Li ya gabatar da hanyoyi guda uku. Da farko ya ce kamata ya yi a rage ikon dake hannun gwamnati, na gudanar da wasu ayyukan da ba sa karkashin ikonta. Na biyu, a kara baiwa kamfanoni iko a wasu fannoni. Na uku kuma a tabbatar da nauyin dake kan gwamnati na kulawa da kasuwanni.

A watanni 6 na farkon shekarar bana, tattalin arzikin kasar Sin ya fuskanci kalubale na raguwar saurin bunkasuwa, amma duk da haka, ya gudana yadda ya kamata, inda karuwarsa ta kai kashi 7.4 cikin 100.

Ana iya tambayar hanyar da gwamnatin kasar ta Sin za ta bi a karshen rabin shekarar da muke ciki, wajen cimma burinta na samun ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Game da wannan, firaminista Li ya bayyana cewa,

"A cikin watanni hudu na karshen shekarar bana, za mu dora muhimmanci kan tabbatar da samun bunkasuwa yadda ya kamata, da inganta yin gyare-gyare, da kyautata tsarin tattalin arziki, da samar da alheri ga al'umma, da kuma hana aukuwar wasu hadarori. Kazalika kuma za mu kara kyautata samar da dabarun inganta matakan da ake dauka daga manyan fannoni, da inganta yin gyare-gyare kan tsare-tsare."

Bugu da kari, firaminista Li ya ce gwamnatin kasar Sin za ta kara karfinta na rage hukumominta, da kuma samar da iko ga masana'antu, da zurfafa gyare-gyare kan haraji, da tsarin kasafin kudi. Kana kuma za a kyautata hanyoyin samar da kayayyakin bukatun jama'a, da kara nuna goyon baya ga sabbin masana'antu, da kara samar da moriya kan harkokin da suka shafi kauyuka, da aikin gona, da manoma.

Shugabanni da dama na wasu kasashe, da na masana'antu da kafofin watsa labaru, da yawansu ya haura 1000 sun saurari jawabin da firaminista Li ya gabatar. Shugaban dandalin na tattauna batun tattalin arzikin duniya Klaus Schwab ya bayyana cewa, yawan mutanen da suke halartar dandalin na wannan karo ya nuna cewa, ayyukan da kasar Sin ke gudanar na inganta yin gyare-gyare na jawo hankalin duniya kwarai.

"Firaminista, dukkanmu mun sausari bayananka. A wannan wuri akwai shugabannin masana'antu fiye da 1000 da suka fito daga kasuwannin ketare, wanda hakan ke nuna cewa muna da imani game da kasarka, kana kasar Sin tana kara jawo hankalin masana'antun ketare." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China